16 Faburairu 2022 - 19:44
Hizbullah : Itace Ke Kera Makaman Roket Da Jiragen Sama Marasa Matuki Da Kanta

Babban sakatare Janar din kungiyar Hizbullah dake kasar Labanon Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa dakarun kungiyar ne ke kera dukkan makaman roka da jiragen sama marasa matuki da kansu ba da taimakon wani ba, kuma suna da karfin da zasu iya bayar da roket ya koma makami mai linzami

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA -Sayyid Nasrullah ya fadin haka ne a wani bayani da yayi ta gidan talabijin a yau Laraba, lokacin da yake bayani kan shuwagabanni da gwamnatin yahudawan Sahyuniya game irin karfin soji da kungiyar ta ke dashi, yace makiya suna yi wa mutane da yaki ne kawai amma sun san cewa yana da matukar wahala garesu kuma zai ja musu mummunar Asara, kuma hizbulla za ta iya inganta makaminta na roka domin kawo karshen barazanar isra’ila

Da yake bayani game da tunawa da zagayowar shahadar shuwagabanin kunfiyar ta hizbullah shahid Ragib Harab da kuma Sayyid Abbas Al’musawi da Imad Mugniya yace yanzu kungiyar ta ci shekaru 40 da kafuwa jinan shahidai da aka zubar ya kara musu karfin guiwa da jajircewa akan hanyar gwagwarmaya.

Daga karshe ya nuna cewa akidar tsayin daka da gwagwarmya a yankin ta fara ne tun kafin kafa kungiyar ta Hizbullah, kuma yayi tir da wasu kasashen larabawa da suka kulla hulda da Isra’ila, kuma ya siffata ta a matsayin gwamnatin wucin gadi da ta kama hanyar rushewa.

342/